Mutanen da basa ajiye kudi a banki sun kai miliyan 28 a Nigeria

0
93

Babban Bankin kasa CBN ya ce akwai al’ummar Nigeria sama da miliyan 28 da basa yin mu’amala da banki wajen ajiye kudi.

Bankin yace yawancin mutanen sun kasance masu yin rayuwa a karkara.

Mataimakin gwamman bankin mai kula da fannin harkokin kudi Philip Ikeazor, ne ya bayyana haka a jiya Talata, inda ya ce, bankin da sauran masu ruwa da tsaki suna aiki domin rage adadin ta yadda za a samar da hanyoyin mu’amala da bankuna ga jama’a.

Binciken bankin CBN yace mafi yawancin wadanda basa amfani da bankuna sun kasance mata ne da matasa wanda suke yin kananun sana’o’i a kauyuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here