Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC tace masu Sana’ar kwangila za’a dorawa laifi wajen yawan lalacewar wutar lantarkin Nigeria.
Hukumar tace hakan ya samo asali akan yadda ake yin amfani da kayan gyara marasa inganci a lokacin gyara wutar hakan ke sawa bayan gyaran da lokaci kankani wutar take sake komawa gidan jiya.
EFCC ta ce jabun na’urorin samar da lantarki da ake amfani da su ne babban musabbabin dauke wutar da ta ta’azara a kwanakin nan.Shugaban Hukumar, Olukoyede, ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi tawagar kwamitin dake yaki da cin hanci ta Majalisar wakilai.
Ya bayyana cewa binciken da hukumar ta gudanar ya gano ya cewa yawancin ’yan kwangilar da ke ake ba wa aikin samar da na’urar lantarki a Nijeriya, ba mai inganci suke sayowa ba.
Yace duk wanda ya kalli sakamakon binciken da EFCC tayi a fannin lantarki sai ya zubar da hawaye.
Yace ingancin na’urorin samar da wuta da ’yan kwangilar suke sayowa bai fi rabin ingancin da ake buƙata ba, wanda shi ya sa wutar take yawan ɗaukewa ko kayan su kone.
Ya ce hukumar EFCC ta ƙudiri aniyar yin aiki tare da majalisar domin yi wa tufkar hanci.