Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC tace cututtukan zazzabin Lassa da Sankarau, sun yi ajalin mutane 762, a fadin Nigeria bayan da suka kamu, a tsakanin shekarun 2023, zuwa 2024.
Shugaban Cibiyar Dr. Jide Idris, ne ya sanar da hakan ranar Talata a Abuja, lokacin da yake jawabi akan barkewar cutukan Lassa da Sankarau a Nigeria.
Yace mutane 361, ne suka mutu bayan kamuwa da cutar Sankarau a kananun hukumoni 174, cikin jihohi 23, da birnin tarayya Abuja, sai zazzabin Lassa daya kashe mutane 401 a jihohi 28.
A cewar NCDC mutane 4,915 ake zaton sun kamu da cutar Sankarau inda aka tabbatar da cewa mutane 380, ne suka kamu.
Shugaban Cibiyar ta NCDC yace suna daukar matakan yakar cutukan wanda yace zuwa yanzu sun yiwa mutane fiye da miliyan 2 rigakafin Sankarau a jihohin Jigawa da Bauchi.