An fara shirin bukukuwan binne gawar tsohon babban hafsan sojojin kasa na Nigeria

0
44

An kawo gawar tsohon shugaban sojojin Nigeria Taoreed Lagbaja, Filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na Murtala Muhammad.

Wannan yana daga cikin shirye-shiryen kai gawar birnin tarayya Abuja inda za’a binne shi a can.

Shugaban kasa Bola Tinubu, ne ya bayar da umarnin gudanar binne gawar Lagbaja bisa girmamawar da ake yiwa wadanda suka hidimtawa Nigeria.

Manyan jami’an sojoji ne suka karbi gawar ta Lagbaja, wanda ya mutu a ranar 5 ga Nuwamba a jihar Legas.

Za’a fara rera wakokin binne Taoreed Lagbaja, a yau da misalin karfe 5 zuwa 7 na yamma, a Abuja, yayin da za’a binne shi a gobe juma’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here