Binciken manyan mutane ya jefa jami’an ICPC cikin barazanar tsaro

0
42

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da dangogin su ta Nigeria, ICPC Dr. Muhammad Adamu Aliyu, ya bayyanawa majalisar dattawa cewa jami’an hukumar dake binciken manyan mutane suna fuskantar kalubalen tsaro da kuma yi musu barazana.

Ya bayyana hakan ga kwamitin majalisar dattawan mai kula da harkokin yaki da cin hanci da rashawa, lokacin da yake zayyano irin nasarorin da hukumar ICPC ta samu a shekarar data gabata, sannan yace suna bukatar karin jami’an tsaro da zasu kara inganta musu aiki.

Yace akwai babban kalubalen da suke fuskanta musamman in aka zo batun binciken yan siyasa, wanda a wasu lokutan mahukunta ke kokarin dakile sahihancin gudanar da bincike.

Yace suna bukatar jami’an tsaro da zasu gudanar da aiki babu shakku kamar yanda ake bawa wasu hukumomin makamantan ICPC.

Dr. Muhammad Adamu Aliyu, yace sun samu nasarori a shekarar data gabata, duk da cewa suna da karancin kudin gudanarwa.

Haka zalika yace suna da ofisoshi, a jihohi 21 amma suna da karancin ma’aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here