Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nigeria EFCC ta kwace fasfon tafiye tafiye na tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, bisa zargin sa da karkatar da Naira Tiriliyan 1 da biliyan dari 3, mallakin jihar a lokacin Mulkin sa.
Hukumar EFCC dai ta kama Okowa tun a ranar 4 ga watan Nuwamba.
Sai dai ya musanta zargin da EFCC ke yi masa na Sace dukiyar Jihar Delta.Bayan shafe lokaci a hannun jami’an hukumar EFCC Okowa, ya shaki iskar yanci bayan da ya cika sharudan belin da aka gindaya masa, cikin su har Mikawa hukumar fasfo din sa.
Da yake mayar da martani kan zarge zargen, Okowa ya bayyana su a matsayin yarfen siyasa da kuma kokarin bata masa suna.
Okowa ya ce ya hidimtawa jihar Delta da gaskiya da riƙon amana a lokacin da yake gudanar da mulkinsa.
Okowa ya kasance dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP a shekarar 2023.