Gwamnatin Kano zata mayar da kananun yara masu yawo a tituna garuruwan su

0
51
Daurawa

Gwamnatin Kano ta kaddamar da wani kwamiti da zai yi aikin kwashe kananun yaran da ke yawo a titunan birnin babu dalili.Gwamnatin tace daukar matakin ya zama wajibi, saboda kyale yaran suna yin yawo a tituna barazana ne ga tsaro.

Kwamitin zai kuma bai wa gwamnati shawara akan yadda za a mayar da yaran garuruwan su na asali.

Kwamitin da zai yi aiki a kasan kwamandan rundunar Hisba, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa zai bi diddigi tare da lalubo yaran da suke yawo a tituna suna kwana a kasuwanni a sassan birnin Kano domin samar musu da kyakkyawar makoma da kuma maslahar al’umma.

Sheik Daurawa ya ce ba za a bayyana yaushe za a fara wannan aiki ba domin ka da wadanda ake son a taimakawa su tsere a gaza cimma manufar aikin.

Sai dai ‘yan kungiyoyin da ake aikin kare kananan yara na ganin akwai bukatar gwamnati ta lura da wasu mahimman abubuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here