Sojoji sun kori mayakan Lakurawa daga sansanin su na Kebbi

0
65

Sabbin yan ta’addan Lakurawa sun gudu daga inda suka yi sansani a Jihar Kebbi bayan sojoji sun kai musu farmaki.

Sojojin sun ragargaji Lakurawan ne yan kwanaki bayan sun hallaka mutane17 a garin Mera da ke Karamar Hukumar Augie tare da sace dabbobi.

Mai magana da yawun gwamnan Kebbi, Abdullahi Umar Zuru, ya ce Bayan harin ne sojoji suka isa yankin, inda suka Fatattaki mayakan.

Zuru ya ce sojojin sun yi nasarar fatattakar mayakan tare da kwato dabbobi da dama da suka sace.

Lakurawa dai wasu sabbin yan ta’adda ne da suka shiga jihohin Kebbi da Sokoto tare da fara kashe mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here