Bashin da ake bin Nigeria ya kusa kaiwa Dala biliyan 43.Bayanin hakan ya fito cikin wani rahoto da ofishin kula da basuka na Nijeriya (DMO), ya fitar.
Ya ce bashin da ake bin Nijeriya a karshen watan Yunin 2024, ya haura dalar biliyan 42.9, kwatankwacin naira tiriliyan 71,826,183,000,000.
Cikin basukan da ake bin Nijeriya, akwai na gwamnatin tarayya da ya kai dala biliyan 38, inda jihohi da babban birnin tarayya ake bin su bashin dala biliyan 4.89, wanda shi ma kwatankwacinsa ya kai naira tiriliyan 8,187,180,300,000.
Sannan akwai wasu basukan cikin gida da ake bin jihohi da ya kai naira tiriliyan 4.27.
Sai Kuma bashin bankin Duniya da kuma Asusun bada Lamuni (IMF) da suka kai dala biliyan 17.13, sai kuma na Tarayyar Turai da ya kai dala biliyan 15.12.
Sauran daidaikun kasashen duniya da kuma bankuna su kuma suna bin Nijeriya bashin dala biliyan 5.49.
A bashin da ake bin jihohin Nijeriya, Jihar Legas ce ke kan gaba, inda kudin da ake binta ya haura dala biliyan 1.2, sai kuma Jihar Kaduna da ke biye ta mata da bashin dala miliyan 640.99.