Majalisar shari’a ta umarci a kori manyan alkalai saboda yin karya

0
28

Majalisar kula da harkokin shari’a ta Najeriya ta bayar da shawarar yi wa wasu manyan alkalai biyu ritayar dole saboda laifin yin Æ™arya a shekarunsu na haihuwa.

NJC ta ce ta gano AlÆ™alin AlÆ™lai na jihar Imo T. E. Chukwuemeka Chikeka, da shugaban kotunan shari’ar Musulunci na jihar Yobe Babagana Mahdi sun aikata laifin yin karyar.

Haka zalika majalisar ta ɗauki mataki kan wasu alƙalan da suka haɗa da yin gargaɗi, da hana su albashi, da kuma saka musu ido bisa laifuka daban-daban da suka aikata.

A cewar sanarwar, da majalisar ta fitarbbincike ya gano alÆ™alin alÆ™alan na Imo na da ranakun haihuwa biyu na 27 ga watan Oktoban 1956 da 27 ga Oktoban 1958, yayin da shi kuma shugaban kotunan shari’a na Yobe yake da kwanan wata har uku daban-daban.

Bisa wannan dalili ne majalisar ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Imo shawarar yi wa Mai Shari’a Chikeka ritayar dole tare da Æ™wace albashin da ya karÉ“a tun daga ranar 21 ga watan Oktoban 2021.

Kazalika, majalisar ta bai wa gwamnatin jihar Yobe shawarar yi wa Mai Shari’a Babagana Mahadi ritaya, wadda ya kamata ya yi tun shekara 12 da suka wuce, sannan kuma ya dawo da albashin da ya karÉ“a na tsawon waÉ—annan shekarun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here