EFCC na kokarin bankado masu siyar kuri’a a zaben gwamnan Ondo

0
47

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nigeria, EFCC na sanya idanu kan masu yunkurin sayen kuri’a a zaben gwaman Ondo da ke gudana yau.

Kamar yadda aka saba gani a zabukan Nigeria, mafi yawancin jam’iyyun siyasa na yin amfani da kudade, da sauran kayan amfani da suka hadar da abinci ko sauran kayan masarufi, wajen siyan kuri’ar masu zabe don samun nasara.

Haka ne yasa jami’an EFCC ke yin basaja, a cikin masu zaben don bankado masu aikata irin wadannan laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here