Har yanzu ba’a ga amfanin sauyin tattalin arzikin da gwamnatin Nigeria keyi ba—-IMF

0
58
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Wani rahoton da asusun bayar da lamuni na duniya IMF ya fitar a baya bayan nan, ya nuna cewa har yanzu ba’a samu wani abun amfani ba, daga sauye sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Nigeria ke aiwatarwa ba, kusan watanni 18.

An fitar da rahoton a makarantar horas da kasuwanci dake jihar Legas, wanda mataimakiyar daraktan IMF Catherine Patillo, tace an samu sakamakon da ake bukata a sauye sauyen tattalin arzikin wasu kasashen Afrika da suka hadar da Cote D’Ivoire da Zambia, sai dai ba’a saka sunan Nigeria cikin wadanda suka samu nasarar sauye sauyen tattalin arzikin ba.

Rahotan ya bayyana cewa yanayin habbakar tattalin arzikin kasashen yakai kaso 3.6, sai dai Nigeria ta tsaya akan kaso 3.19.

Nigeria dai ta fara aiwatar da wasu sauye sauyen tattalin arziki tun farkon mulkin shugaban kasar Bola Tinubu, wanda suka hadar da cire tallafin man fetur, cire tallafin sauyin kudaden ketare, cire tallafin aikin Hajji, da yunkurin kara harajin VAT da sauran karin abubuwan da suka danganci karin kudin wutar lantarki

Amma har yanzu an gaza samun amfanin hakan saboda al’ummar kasar na kara shiga kuncin rayuwa da tsadar rayuwa saboda karyewar darajar Kudin kasar wato naira.

Bayan haka shugaban kasar Bola Tinubu, yace bazai saurara ba har sai ya cimma burin sa akan sauyin tattalin arzikin da ya faro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here