Manyan mutane daga fadin Nigeria sun halarci daurin auren yar Sanata Kwankwaso

0
68

Manyan mutane da suka hadar da Malamai, yan siyasa, masarauta, yan kasuwa, da sauran su, ne suka halarci taron daurin auren yar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da dan fitaccen dan kasuwar nan Dahiru Mangal, a yau asabar.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, da tsohon Shugaban Ƙasar Nigeria Olusegun Obasanjo, da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar duk sun halarci bikin auren da akayi a jihar Kano.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, tare da mataimakinsa, Aminu Gwarzo, sun karbi bakuncin manyan baki a filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano kafin su wuce Fadar Sarkin Kano inda aka daura auren.

Cikin wadanda suka halarci taron akwai tsoffin gwamnoni guda bakwai, ciki har da Lucky Igbinedion da Isa Yuguda, wanda suka zo Kano tun ranar Juma’a.

Haka zalika, Gwamnan Jihar Katsina Umar Dikko Radda ya zo daurin auren, da kuma manyan malaman Islama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here