An kashewa jihohin Arewa naira biliyan 45 don ragewa al’ummar su talauci

0
54

Wani rahoton jaridar Punch, ya bayyana yadda aka ce an kashewa jihohin Arewa naira biliyan 45, cikin watanni 6 da manufar rage talaucin da yankin ke ciki, da tsadar rayuwa.

A ranar juma’ar data gabata hukumar kididdiga ta kasa NBS tace yanayin hauhawar farashin kayyakin masarufi ya kai kaso 33.88 a watan Octoba, wanda a watan Satumba ya tsaya akan kaso 32.70.

A watan junairu kuwa hauhawar farashin tana kan kaso 29.90

Duk da wannan kudade da ake cewa ana warewa don rage yawan talauci a arewa hakan baya yin tasiri, saboda matsalolin cin hanci da rashawa, da kuma masu wawure dukiyar da ake kokarin samarwa da mutane sauki.

Jihohin arewacin Nigeria sun fi shiga matsalar kangin talauci da fatara, inda a watan Afrilu mai bawa shugaban kasa shawara a fannin tsaro Ribadu, yace arewa tana fama da talauci musamman arewa ta yamma, wanda yankin yake da kaso 40.1 cikin dari na yawan matalautan Nigeria.

Binciken ya nuna cewa jihar Sokoto ce kan gaba a yawan mutanen dake fama da talauci, sai Zamfara, Yobe, Bauchi,Kebbi, Katsina,Gombe,Kano,Taraba,Borno,Niger, da kuma Adamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here