An wawure dala miliyan 32 da za’a yi amfani da su wajen samar da ruwan sha a Nigeria

0
50

Bankin Duniya ya bankado yadda aka nemi dala miliyan 32 aka rasa a Nigeria wanda aka tsara yin amfani da su wajen samar da ruwan sha mai tsafta ga al’ummar kasar.

Bayanin bankadowar ya fito cikin wani rahoton bankin na saka takunkumi da ake fitarwa Shekara bayan shekara wanda bankin ke fitarwa.

Rahotan yace an tsara za’a yi amfani da kudin wajen inganta ayyuka a Nigeria, sai dai ba’a yi hakan ba.

Bayan gano wannan danyen aiki bankin na duniya ya dauki aniyar nemo inda aka kai kudaden ta hanyar tattaunawa da wakilan gwamnatin Nigeria akan aikin da aka shirya za’a yi da kudin, da kuma shugabannin fannin sanin harkokin kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here