Shugaba Tinubu yana ganawa da Fira ministan India a Abuja

0
57

A yanzu haka shugaban Nigeria Bola Tinubu, yana kan ganawa da Fira ministan India Nerendra Modi, a fadar shugaban kasar dake birnin tarayya Abuja.

Modi, wanda ya sauka a Nigeria, da daren ranar asabar, ya zarce zuwa fadar shugaban da misalin karfe 10:20, wanda ya samu tarba daga Tinubu.

Lokacin da Modi, sauka a Nigeria an karbe da saka taken kasar India don nuna girmamawa a gare shi, tare da yi masa faretin ban girma.

A halin yanzu da shugabannin suke ganawar sirri ana sanya ran zasu saka hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da sauran su.

Modi, shi ne fira ministan India daya ziyarci Nigeria tun bayan Manmohan Singh, daya ziyarci kasar a shekarar 2007

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here