Bamu yanke hukunci akan dokar haraji ba—- Majalisar wakilai

0
62

Shugaban majalisar wakilai Tajuddeen Abbas, yace har yanzu basu yanke wani hukunci akan kudirin yin kwaskwarima a fannin karbar haraji ba.

Abbas, ya sanar da hakan a yau lokacin da majalisar ta fara yin magana akan kudirin dokar wadda shugaban kasa Tinubu ya aike mata.

A cewar sa, majalisar zata yi aikin dake kanta na dubawa tare da yin gyara a inda ake bukatar yin hakan a cikin kunshin dokar.

Kudirin dokar ya kunshi duk wani fannin karÉ“ar haraji na Nigeria, wanda za’a yi musu gyare-gyare kamar yadda shugaban kasar ke niyyar kara yawan harajin da yan Nigeria ke biya.

Shugaban Nigeria ya mikawa majalisar kudirin dokar harajin, duk da cewa majalisar zartarwa ta kasa ta nemi a janye kudirin saboda tun yanzu ya fara haifar da cece-kuce, sai dai shugaban kasar yace bazai Janye aniyar sa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here