Tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo, ya nemi a gaggauta yiwa tsarin gudanar da zaben kasar garambawul.
Obasanjo, ya nemi hakan lokacin da yake jawabi a jami’ar Yale dake kasar Amurka, inda ya fito fili yace akwai bukatar a kori shugaban hukumar zabe INEC Farfesa Mahmud Yakubu, da sauran ma’aikatan hukumar a dake kowanne mataki.
Obasanjo, ya ayyana zaben shekarar 2023, a matsayin wanda yake cike da cin amana, yana mai jaddada cewa tabbas akwai bukatar yin gyara a INEC don inganta harkokin zabe ta yadda za’a rika yin sahihin kuma amintaccen zabe a Nigeria.
Haka zalika yace akwai bukatar rage wa’adin shugabannin hukumar zaben, da Kuma kaucewa yin son zuciya wajen nada shugabannin.
Bayan haka, Obasanjo, ya nemi a rika tantance wanda ake son bawa shugabancin INEC, da wadanda za’a bawa manyan mukamai, inda yace wannan ce kadai hanyar da za’a bi don samun sahihan shugabannin hukumar.