Rashin mai a mota ya hana jami’an kwana kwana zuwa kashe gobara a Jos

0
52

Wata gobara data tashi ta janyo asarar makudan kudade a kasuwar Laranto dake Jos a jihar Filato.

Wutar ta tashi da misalin karfe 11 na daren jiya bayan an tashi daga cin kasuwar.

Shugaban kungiyar yan kasuwar, Alhaji Idris Shehu, ya tabbatar da cewa gobarar ta cinye bangaren ’yan katako da bangaren masu sayar da kayan daki.

Sai dai yace har yanzu ba’a kai ga sanin dalilin tashin gobarar ba.

Shugaban sashin yan katako na kasuwar, Umar Aliyu, ya ce jami’an kashe gobara basu kawo dauki akan lokaci ba.

Ya ce lokacin da aka kai wa jami’an rahoto, ba su zo ba, inda suka ce babu mai a motocinsu.

Yace Sai bayan da Shugaban Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa da Kwamishinan Ruwa suka zo kasuwar, suka kira jami’an kwana-kwanan da ke gidan Gwamna, sannan suka kawo ɗauki suma kashe gobarar.

Ko a shekarar 2023, sai da makamanciyar Gobarar ta tashi a kasuwar ta Laranto dake Jos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here