Tsoho mai shekaru 60 ya mutu bayan fadawa rijiya a Kano

0
58

Wani tsoho mai shekaru 60 ya rasu bayan ya fada rijiya a jihar Kano.

Mutumin wanda yake Sana’ar tukin mota ya gamu da wannan iftila’i a kan titin zuwa Hadeja daga Kano.

Dattijon, mai suna Sabi’u Unguwa Uku, wanda direban matar wani tsohon minista ne ya gamu da ajalinsa a rukunin gidajen ma’aikatan Babban Bankin kasa (CBN) da ke kan titin Hadeja.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi ya ce tsautsayi ya ritsa da direban bayan da ya sauke wasu baƙi a wani gida da ke kusa da abin ya faru.

Abin ya faru lokacin da mamacin zai yi fitsari, ashe akwai rijiya a wajen da yayi niyyar fitsarin wanda ba tare da ya sani ba ya afka cikin tsohuwar rijiyar da aka dena amfani da ita.

Ya ce bayan samun kiran gaggawa kan lamarin jami’an hukumar sun isa wajen suka ceto mutunin, suka kai shi Asibitin Sir Sanusi, inda likita ya tabbatar cewa ya rasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here