Yan ta’adda sun kashe manomi tare da yin garkuwa da yan uwansa a Taraba

0
60

Yan bindiga sun kashe wani manomi tare da sace karin mutane 6 a karamar hukumar Garbatau, Bali, dake jihar Taraba.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutumin mai suna Alhaji Wanda Maibultu, a karshen mako lokacin da yake aiki a gonar da.

Maibultu, ya kasance babban dan kasuwar kayan amfanin gona.

Jaridar Daily trust, ta rawaito cewa garin da akayi garkuwa da mutanen ya kasance a tsakanin wasu tsaunika biyu.

Wani mazaunin kauyen Maihula, mai suna Adamu Dauda, yace yan ta’addan sun nemi iyalan wadanda aka yi garkuwar dasu su biya kudin fansar yan uwan su, akan naira miliyan 100.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, bai yi Karin bayani akan faruwar lamarin ba, sakamakon zuwa rubuta Wannan labari bai yi karin bayani akan sakon da aka tura masa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here