Yau ce ranar fara yin rigakafin kyandar Biri a Nigeria

1
91

Yau litinin 18 ga watan Nuwamba itace ranar da aka tsara domin fara yin rigakafin kyandar Biri a Nigeria.

Za’a fara yin rigakafin kyandar Birin a wasu jihohi 7 na kasar, wanda haka ne yasa Nigeria zata zama kasa ta uku da aka fara yin rigakafin bayan kasashen Rwanda da Jamhuriyar DumukuraÉ—iyyar Kongo.

Ma’aikatar lafiya ta ce za a fi mayar da hankali a kan Ma’aikatan lafiya da sauran jama’a da ke cikin hadarin kamuwa da cutar.

Tun a watan Ogusta Nigeria ta karbi alluran rigakafin kashin farko da aka bawa wasu kasashen Afrika, bayan ayyana cutar kyandar Biri a matsayin annoba da hukumar lafiya ta duniya tayi.

Kasar Amurka ce ta bai wa Nigeria allurar sanfurin Jynneos (MVA), 10,000.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutune 118 sun kamu da cutar a jihohi 28 da birnin tarayya Abuja.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here