Mahukuntan kasar Burtaniya sun kulle wasu daliban Nigeria su 4 masu yin karatu a kasar bayan samun su da laifin yin rigima da wuka, a ranar 4 ga watan Nuwamba, na shekarar 2021 a birnin Leicester.
Lamarin daya faru akan titi yayi sanadiyyar jikkata wani dan shekaru 18, da yaji munanan raunuka da sai da aka kai shi asibiti domin kulawa da lafiyar sa.
Karanta karin wasu labaran:Nigeria zata ciyo bashi saboda siyo jiragen yaki
An samu nasarar kama yan Nijeriyar bayan samun bayanan na’urar daukar hoto da ake sakawa akan tituna da kuma bibiyar wayoyin su da akayi, wanda haka ne yasa aka gurfanar dasu a gaban kotu.
Shari’ar da aka shafe makonni 6 ana yi an kammala ta a ranar 14 ga watan da muke ciki.
Yan kasar Nijeriyan da aka daure sun hadar da Destiny Ojo, mai shekaru 21, wanda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 7, sai Habib Lawal, shima ai shekaru 21, da aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 5, yayin da aka yankewa Ridwanulahi Raheem, hukuncin zaman yarin shekaru 3, da kuma Joshua Davies, sai daurin shekaru 2.