Yan majalisar arewa sun nuna damuwa akan kudirin dokar haraji

0
55

Mambobin majalisar wakilai da suka fito daga yankin arewacin Nigeria, sun nuna damuwa akan kudirin dokar haraji dake gaban majalisar don neman sahalewa.Sun bayyana damuwar tasu a jiya litinin, yayin da majalisar ke tattaunawa kan kudirin dokar harajin wadda shugaban kasa Tinubu ya aikewa musu.

Babban abin da ya kawo cece kuce a cikin dokar shine yanda ake neman sauya jadawalin rarraba harajin siyan kayayyaki wato VAT, wanda ake kyautata zaton ana son yiwa arewa zagon kasa a cikin kunshin dokar.

Karanta karin wasu labaran:Shugaban Nigeria Tinubu zai halarci taron G20

Kudirin dokar ya kunshi duk wani fannin karɓar haraji na Nigeria.

Saboda cece-kuce dake tattare da dokar majalisar tattalin arziki ta kasa ta nemi a dakatar da aiwatar da wannan abu, sai dai shugaban Nigeria Tinubu, ya ce babu abinda zai hana shi turawa majalisar neman sahalewa akan kudirin.

Wasu daga cikin yan majalisar jihohin Filato, Borno, da Adamawa, na daga cikin wadanda ke bayyana adawar su da wannan kudiri da aka tabbatar zai yiwa yankin arewa zagon kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here