An kama dan kasar Aljeriya mai yin safarar makamai a jihar Sokoto

0
62

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Zamfara Mohammed Dalijan, ya bayyana cewa jami’an su sun yi nasarar kama wani mutum mai shekaru 58, da zargin yin safarar miyagun makamai a Sokoto mai fama da tashin hankalin yan fashin daji.

Kwamishinan ya bayyana hakan a jiya talata lokacin da yake yin jawabi a Gusau babban birnin jihar.

Bayan haka ya ce ’yan sanda sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 16, yayin samame daban-daban da suka kai cikin makonni uku da suka gabata.

Hakazalika, yace sun samu wasu manyann bindigogi guda biyu da wata bindiga ƙirar gida daga hannun wani mai ƙera makamai a Jos.

Har ila yau rundunar yan sandan ta Zamfara ta ƙwato harsasai, da kuɗi Naira miliyan 2.5, da wasu kayayyaki daga hannun wasu bata gari masu aikata lefuka daban daban.

A wani cigaban yan sandan sun kama masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba tare da ƙwato injinan haƙar ma’adinai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here