Jami’an Civil Defence sun Kashe yan Boko Haram 50 a Kaduna

0
52

Akalla yan ta’addan Boko Haram 50 jami’an tsaron al’umma na farin kaya civil defense, suka kashe bayan musayar wuta data faru tsakanin jami’an da yan ta’addan a jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar NSCDC Babawale Afolabi, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar a jiya Talata, yana mai cewa jami’an su sun dakile harin kwantan bauna da yan Boko Haram suka kai musu a yankin Farin-kasa, ranar litinin.

Yace yan Boko Haram sun kaiwa jami’an NCDC dake tsaron wajen samar da wutar lantarki a yankin Shiroro hari, a jihar Niger.

Babawale, yace bayan harin na yan ta’addan na Boko Haram, jami’an su sun samu nasarar dakile harin, tare da kashe 50, daga cikin bata garin, da suka zarce su 200.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here