Yan ta’adda sun sace mai unguwa a birnin Gwari

0
65

Wani mai unguwa a karamar hukumar Birnin Gwari ya gamu iftila’in yin garkuwa daga bangaren yan fashin daji.

Yan fashin dajin sun Kuma kashe ’yan banga hudu, a wani harin da suka kai, birnin Gwari dake Kaduna.

Yan fashin dajin sun kuma ƙona babura bakwai tare da sace wasu baburan biyar a harin da suka kai Unguwar Agyaro da ke Kakangi.

Tsohon Shugaban Ƙungiyar Masu Kishin Yankin Birnin Gwari, Ishaq Usman Kasai, ya tabbatar cewa yan bindigar sun yi awon gaba da mutane huɗu a yankin Maraban Agyaro.

Shima dan majalisar dake wakiltar Kakangi a majalisar dokokin Kaduna, Yahaya Musa DanSalio, ya ce ya samu labarin mutuwar ’yan banga uku da ɓacewar wani guda.

Sannan yace an sanar da gwamnatin Kaduna jihar faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here