Za’a bawa yan Nigeria mazauna ketare damar kada Kuri’a lokacin zabe

0
38

Za’a iya cewa yan Nigeria mazauna kasashen duniya daban daban sun kusa samun yancin zabar shugabanni daga inda suke ba sai sun zo kasar ba a lokacin da ake gudanar da zabe.

Yan Nigeria mazauna ketaren zasu samu wannan dama da zarar majalisun dokokin kasa sun kammala amincewa da kudirin neman bukatar hakan.

Karanta karin wasu labaran:An yi artabu tsakanin Bello Turji da sojojin Nigeria

Wannan kudiri da zai bayar da hanyar yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima domin bai wa ƴan ƙasar mazauna ƙasashen waje damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓe ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai a yau Laraba.

Kakakin majalisar wakilai Abbas Tajudeen da wani dan majalisar mai suna Sadeeq Abdullahi, ne suke goyon bayan samar da dokar bawa yan Nijeriyan damar yin zabe daga wata kasa.

An amince da karanta ƙudurin karo na biyu a watan Yuli, kuma an miƙa shi ga kwamitin da ke kula da harkokin zabe don ci gaba da nazari akai.

Sai dai bayan tsallake karatu na biyu a ranar Talata, an kuma tura kudirin zuwa ga kwamitin gyaran kundin tsarin mulki don ci gaba tattaunawa a kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here