An kama jagoran masu son kafa kasar Biafra

0
69

Jami’an tsaron kasar Finland sun kama jagoran haramtacciyar Kungiyar masu son kafa Biafra daga kasar Nigeria, IPOB, mai suna Simon Ekpa, bisa zargin sa da aikata ta’addanci.

An samu labarin kamen nasa bayan da kafofin yada labarai daga Finladn suka ruwaito cewa wata kotu a yankin Päijät-Häme ta tura Ekpa gidan yari bisa zarginsa da tunzura mutane su aikata laifukan ta’addanci.

Karanta karin wasu labaran:::Kashim Shettima yace Nigeria ta fara fita daga lalacewar tattalin arziki

Kotun ta ce Simon Ekpa, yana yin amfani da shafukan sada zumunta wajen yada labaran da bana gaskiya ba don cimma wata manufar sa.

Ekpa, wanda ɗan Najeriya ne, mai shaidar zama ɗan ƙasar Finland, an haife shi ne a shekarar 1985, kuma ya taɓa bayyana cewa yana jagorantar wata ƙungiya a Najeriya da take fafutikar kafa ƙasar Biyafara.

Ƴansanda sun ce suna zargin Ekpa da yaɗa manufofin sa daga ƙasar ta Finland, don tayar da tarzoma a Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here