Gwamnatin Kano ta mayar da yan zanga-zanga zuwa hannun iyayen su

0
53

Gwamnatin jihar Kano, ta kammala kula da lafiyar kananun yaran da gwamnatin tarayya ta kama lokacin zanga zangar tsadar rayuwa, wanda aka sake su su 76, bayan shafe kusan watanni 3, a hannun jami’an tsaro.

Idan za’a iya tunawa gwamnatin Kano ta karbi yaran daga hannun gwamnatin tarayya tare da cigaba da kula dasu a asibiti ba tare da mika su hannun iyayen su ba, don tabbatar da binciken lafiyar su kafin su shiga cikin al’umma.

Karanta karin wasu labaran:::Kotun duniya ta bayar da umarnin kama Fira-Mininstan Isra’ila saboda kisan Falasdinawa

An killace yaran tare da kula da lafiyar su a asibitin Muhammadu Buhari, dake unguwar Giginyu.

A yau alhamis an yi bikin mika yaran su 76, zuwa hannun iyayen su kamar yadda gwamnatin ta alkawarta.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya tabbatar da cewa duk yaran sun samu kulawar masana lafiya kuma yanzu suna cikin koshin lafiya.

  • A wani cigaban Gidauniyar tsohon gwamnan jihar Sokoto Bafarawa ta tallafa wa yaran da kuÉ—i ₦50,000 kowanne daga cikin su domin su fara sabuwa.
  • Yaran dai sun kasance a hannun Gwamnatin Kano tun ranar 5 ga Nuwamba, 2024, bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sallame su daga tuhumar cin amanar Æ™asa da gwamnatin tarayya ta janye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here