Manufofin Tinubu suna cutar da yankin Arewa—ACF

0
41

Kungiyar tuntuba ta mutanen yankin arewacin Nigeria ACF, tace manufofin gwamnatin shugaban kasar Tinubu, sun kasance masu yin illa ga cigaban al’ummar yankin, yayin da kungiyar ta nemi shugaban ya gaggauta canja matsaya akan matakan da yake dauka masu kawowa yankin koma baya.

Kungiyar ta bayyana hakan cikin wata sanarwar data fitar, tana mai cewa nazarin da tayi akan manufofin Tinubu, ya nuna cewa suna yiwa talakawa illa musamman masu yin rayuwa a arewa dake fuskantar kalubale kala-kala.

Karanta karin wasu labaran:::Darajar Bitcoin daya ta zarce Dala dubu 97

Sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya rabawa manema labarai, ta ce mazauna yankin arewacin Nigeria na fama da tsananin rashin abinci da tsaro da ƙarancin samun damar ilimi da koyan sana’o’i da kuma harkokin kasuwancin da za su dogara da kansu.

Muhammad-Baba yace rayuwar mutanen arewa ta dogara akan Æ™ananan sana’oi, sai dai a yanzu mafi yawancin al’ummar yankin sun rasa madora da kuma shiga kunci saboda matakan sauyin tattalin arzikin da Tinubu, ke dauka ba tare da yayi duba akan irin illar da hakan zai yiwa mutane ba.

Ƙungiyar ta ce duk da yake É—aukar irin waÉ—annan matakai na da matukar tasiri in akayi abun daya dace, amma kuma bai dace hakan ya yi illa ga mutanen da ake cewa ana yi domin su samu sauki ba, saboda wannan hali da ake ciki zai iya hallaka da yawa daga cikin al’ummar Nigeria.

Muhammad-Baba ya ce sun buƙaci shugaban ƙasar da ya sake nazari ta hanyar da zai yi la’akari da rayuwar jama’a, tare da kuma sauraron ƙorafin jama’a domin gyara ga matakan da yake ɗauka waɗanda ke yiwa ƴan ƙasa illa.

Ƙungiyar wadda ta ce ta fahimci ƴan arewa ne kawai za su kare martabar yankin, ta buƙaci samun daidaito wajen raba mukamai da kuma gaggauta samo maslaha dangane da matsalar samar da wutar lantarki da talaucin da ya addabi jama’a da rashin ayyukan yi da kuma koma bayan da yankin ke fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here