Kakakin majalisar dokokin jihar Lagos, Mudashiru Obasa, yace majalisar ba zata yi kasa a gwuiwa ba wajen gaggauta amincewa da kasafin kudin da Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ya gabatar musu ba, wanda ya zarce naira triliyan 3.
Obasa, ya bayyana hakan a jiya Jim kadan bayan Sanwo-Olu, ya gabatar wa majalisar kasafin a jiya alhamis.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa a kunshin kasafin an kiyasta cewa Lagos zata samu kudin shiga da yawan su yakai naira triliyan 2.60, sai sauran fannin da ake sa ran samun naira biliyan 408.92.
Kakakin yace nan gaba kadan zasu fara aikin yin nazari akan kasafin, saboda a cewar sa al’ummar jihar Lagos zasu samu cigaba daga kunshin kasafin.
Kamfanin dillancin labarai NAN, yace za’a kashe naira triliyan 1.239, na amfanin al’amuran yau da kullum, sai naira triliyan 1.766, na ayyukan raya al’umma.