Rikicin manoma da makiyaya ya hallaka mutane a jihar Nassarawa

0
66
Gona - Neja
Gona - Neja

Wani rikici daya faru tsakanin manoma da makiyaya yayi sanadiyyar mutuwar mutane 3 a kananun hukumomin Nassarawa da Toto, dake jihar Nassarawa.

Rikicin dai ya faru a yankin Dogon Dutse.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Umar Nadada ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin 18 data gabata da yamma.

Babban Jami’in ’yan sandan yankin ya bayyana cewa, sun tarar da gawarwaki 2 a gonakin da suka je, sannan wasu mutane hudu sun jikkata.

Bayan rikicin an kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da basu magani.

A wani bincike da ’yan sandan suka gudanar, sun gano wata gawa a cikin daji, wanda hakan ya kawo adadin waɗanda suka mutu zuwa uku.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa an daidaita al’amura a yankin, kuma ’yan sanda na gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin rikicin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here