Rundunar Hisbah ta Kano zata cigaba da kama masu shagunan yin Caca

0
51

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana shirinta na sabunta dokar ta-baci a kan masu bude shagunan caca, biyo bayan hukuncin da kotun kolin Nigeria ta yanke wanda ya soke dokar Caca ta kasa.

Hukuncin, wanda aka yanke ranar Juma’a, ya soke dokar caca ta Æ™asa da aka samar a shekarar 2005, wacce ta kafa hukumar kula da al’amuran caca ta tarayya da halatta yin cacar wasanni da sauarn su.

Hukuncin yace daga yanzu gwamnatocin ne suke da alhakin halastawa ko haramta yin Caca ba gwamnatin tarayya ba.

Babban Daraktan rundunar Hisbah ta Kano, Abba Sufi, yace daga yanzu rundunar zata cigaba da yakar duk wani nau’in caca a Kano, saboda caca haram ce a dokokin Kano, sakamakon cewa gwamnatin tana yin amfani da dokokin addinin muslinci.

Yace a watan daya gabata jami’an rundunar sun kai samame shagunan masu yin caca a kwaryar birnin Kano, tare da rufe shagunan saboda addinin muslinci ya haramtawa duk musulmi yin ta, sai dai an dakatar da samamen sakamakon kalubalantar rundunar da akayi cewa dokar hukumar caca ta shekarar 2005, bata bayar da damar kai samame shagunan yin Caca ba.

Bayan yanke hukuncin Abba Sufi, yace a yanzu kotu ta banbance wanda yake da ikon amincewa ayi Caca tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here