Yan ta’adda sun kashe manoma da kone buhun masara 50 a Niger

0
59

Akalla manoma 7, aka kashe cikin su har da wani dan Bijilanti, tare da kone wata babbar mota mai dauke da buhun masara 50 a Bangi dake karamar hukumar Mariga ta jihar Niger.

Jaridar Daily trust, ta rawaito cewa mutanen sun gamu da ajalin nasu bayan sun je girbin amfanin gona, daga haka ne yan ta’addan suka yi musu kwantan bauna suka kashe su da kuma kone babbar motar da suke ciki.

Majiyar jaridar Daily trust, ta tabbatar da cewa an kashe mutanen lokacin da suke kokarin kawo amfanin gonar da suka shuka gida, wanda maharan suka ki yiwa manoman komai suna kallon su har sai da suka gama dora kayan nasu akan mota sannan suka aikata musu wannan mummunan aiki.

Majiyar tace a yanzu girbe amfanin gona ya zama babbar wahala ga manoman Mariga, saboda tsananin kisan da yan bindiga ke yiwa manoman.

A wani labarin yan ta’adda sun kashe wani mai suna Malam Danjuma, a Kontagora, bayan karbar kudin fansa naira miliyan 20, daga iyalan sa, wanda suka kashe shi bayan shafe makonni uku a hannun su.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here