Dattawan arewa sun kalubalanci kudirin dokar haraji ta Nigeria

0
67

Kungiyar dattawan arewa ta kalubalanci kudirin dokar yin garambawul ga fannin haraji da shugaban Kasa Tinubu ya aikewa majalisun dokokin kasa, inda kungiyar tace dokar zata kasance wata babbar barazana ga hadin kan al’ummar Nigeria da kasar baki daya.

NEF, ta bayyana cewa an samar da kudirin dokar ba tare da tuntubar wadanda suke da ruwa da tsaki ba, musamman majalisar tattalin arzikin kasa.

Shugaban Ƙungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ne ya bayyana hakan bayan taron kwamitin amintattun kungiyar karo na biyu na shekara-shekara da Kungiyar ta gudanar a Abuja.

Kungiyar ta yabawa kungiyar gwamnonin jihohin Arewa da majalisar sarakunan arewacin Najeriya da suka nuna adawa da kudurin, inda suka bayyana matsayarsu a matsayin masu kishin kasa.

Kungiyar ta kuma nemi yan majalisar arewa a majalisar dokokin Nigeria dasu bayyana albarkacin bakin su akan wannna doka.

Taron ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki a Nigeria dokar sake fasalin haraji an yi ta da nufin tursasawa ’yan kasa, kuma hakan barazana ce ga hadin kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here