Obasanjo yace ciwon tari ne ya hana shi shan taba sigari

0
44

Tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo, yace yin ta’ammali da miyagun kwayoyi babbar masifa ce da barazana ga cigaban matasa da al’umma baki daya, inda yace kwayoyi suna lalata rayuwar matasa.

Tsohon shugaban kasar, ya bayyana hakan a Abeokuta, lokacin da yake jawabi a wajen taron yaki da shan miyagun kwayoyi, da wata kungiya ta shirya.

Obasanjo, ya kara da cewa yankin Afrika ta yamma ya kasance wata cibiyar shan miyagun kwayoyi fiye da inda ake tsammani.

A cewar sa sama da shekaru 10 da suka wuce, sun gano cewa Afirka ta Yamma ta zama cibiyar shan ƙwayoyi, kuma lamarin ya ƙara muni tun daga wancan lokacin, zuwa yau.

Ya bayyana fara shan taba sigari da yayi ya haifar masa da matsanancin ciwon tari, wanda hakan ya sa ya bar shan tabar gaba É—aya, sannan yace yana da wahala mutum ya daina ta’ammali da miyagun kwayoyi ko sigari bayan fara yin ma’amala dasu.

Daraktan Asibitin Serenity Royale, Kunle Adesina, wanda shima yayi bayani a wajen taron cewa yayi kashi 14.3% na ‘yan Najeriya suna amfani da ƙwayoyi, inda ya ce mace ɗaya a cikin mutum biyar na amfani da ƙwayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here