Tinubu ya dawo Nigeria bayan halartar taron G20

0
40

Shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo Nigeria bayan halartar taron kungiyar kasashen duniya 20 masu karfin tattalin arziki wato G20, wanda aka yi a kasar Brazil.

Shugaban ya iso Nigeria a cikin daren ranar asabar tare da mai dakin sa Remi Tinubu, wanda suka sauka a birnin tarayya Abuja.

A lokacin taron an tattauna akan batutuwan da suka shafi cigaban duniya musamman tattalin arziki.

Shugaban Nigeria a lokacin taron ya tabbatar da cewa zai yi duk mai yiwuwa don magance matsalar yunwa data addabi al’ummar kasar.

Shugaban ya samu tarba daga jiga-jigan gwamnatinsa da ‘yan siyasa, ciki har da Ministan Abuja, Nyesom Wike da shugaban ma’aikatan fadarsa, Femi Gbajabiamila da shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribado da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here