A jihar Kano an kama Wani mutum mai sace batirin sola a Masallacin juma’a

0
60

Rundunar tsaron al’umma ta farin kaya Civil Defence, ta sanar da kama wani mutum da akayi zargin yana aikata laifin sata hadi da barnatar da dukiyoyin mutane.

Mutumin shine Murtala Aliyu Muhd, mai shekaru 35 a duniya daya fito daga Dawakin Dakata a karamar hukumar Nassarawa, wanda ake zargi da satar batirin Sola na masallacin Juma’a dake unguwar Dakata.

Kakakin rundunar NSCDC, reshen Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi, yace wanda ake zargin ya shiga masallacin ta taga da tsakar dare tare da dauke batirin.

An kama shi washegari a unguwar Yankaba yayin da yake ƙoƙarin kai batirin kasuwa ya sayar dashi.

Bayan haka an zargin wannan mutum da sace zunzurutun kudi har naira dubu dari uku, a wani Masallacin na daban, a lokacin baya.

Rundunar NSCDC tace wanda ake zargin zai fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here