Sojojin jamhuriyar Niger sun kashe mayakan Lakurawa

0
68

Sojojin jamhuriyar Niger sun kashe mayakan Lakurawa

Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da kashe mayakan Lakurawa, da suka shiga kasar ba da jimawa ba.

Mayakan Lakurawa dai sun shiga jamhuriyar Niger ta kudu maso yammacin kasar kamar yadda kafar Tamtan.info ta ruwaito a yau.

Rundunar ta ce sun kashe mayaƙan ƙungiyar a ranar 21 ga Nuwamba a yankin Muntseka, dake Illela kan iyakar Niger da Najeriya.

Rahoton kisan yace yan ta’addan Lakurawa sun kasance wasu sabbin yan ta’adda da suka fito a jihohin arewa maso yammacin Najeriya musamman, Kebbi da Sokoto da suke da iyaka da jihohin Jamhuriyar Nijar na Dosso da Tahoua.

Tun a baya an bayar da rahoton cewa Lakurawa sun kashe mutane 15, bayan bayyanar su.

Lakurawa sun dauki alhakin wasu hare hare da aka yi a jihohin Kebbi da Sokoto, tare da ikirarin alaka da ƙungiyar Ansaru mai samun goyon bayan kungiyar al-Qaeda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here