Yan ta’adda sun yi yunkurin sace mutane a hanyar Katsina

0
57

Jihar Katsina dake daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Nigeria, na cigaba da fuskantar ayyukan ta’addanci da suka hadar da garkuwa da mutane, kisan babu gaira babu dalili, kone amfanin gona, da sauran su, wanda har yanzu jami’an tsaro suka gaza magancewa tsawon shekaru.

Ana tsaka da haka ne rundunar yan sandan jihar ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane tare da kubutar da wasu mutane 14 a yammacin ranar Lahadi.

Lamarin ya afku a kauyen Dan’arau da ke hanyar Magama zuwa Jibia a karamar hukumar Jibia.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar ta Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, yace sun kubutar da mutanen bayan da yan bindiga suka tare hanya tare da bude wuta akan wasu motocin matafiya guda biyu, sannan suka yi yunkurin sace mutanen dake cikin motocin.

Yace yan ta’addan suna yunkurin yin garkuwar ne yan sanda suka samu labari tare da kaiwa mutanen da ake son sacewa dauki, ta hannun shugaban ofishin yan sandan na karamar hukumar Jibiya, har yan sandan suka samu nasarar fatattakar mayakan tare da kubutar da mutane 14, da za’a sace.

Jami’in hulda da jama’ar yace sai dai a yayin artabun, biyu daga cikin mutanen da aka ceto sun samu raunnin harbin bindiga wanda aka kai su su asibiti domin yi musu magani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here