Bankin CBN ya kara kudin ruwa zuwa kaso 27.50

0
52

Babban bankin kasa CBN, ya kara abin da za’a rika biya na kudin ruwa bayan karbar aron kudi zuwa kaso 27.50, wanda a baya ake cajar kaso 27.25, cikin dari.

:Matatar Fetur ta Warri zata fara aiki bada jimawa ba—NNPCL

Kwamitin kula da harkokin kudi na bankin MPC, ne ya sanar da yanke hukuncin kara kudin ruwan, wanda bankin yace hakan baya rasa nasaba da kudirin sa na dakile hauhawar farashin kayayyakin masarufi da yakai kaso 33.88, a watan Oktoba na 2024.

Gwamnan babban bankin Olayei Cardoso, ne ya bayyana hakan cikin wata takardar bayan kammala taron kwamitin ranar Talata a birnin Abuja, sannan yace suna yin haka ne da manufar daidaita tattalin arzikin kasar, da rage hauhawar farashin kayayyaki.

Yace tattalin arzikin Nigeria yana farfadowa a yayin da adadin kudaden da kasar ke ajiyewa a kasashen ketare ya kai dala biliyan 40.88, zuwa ranar 21, ga watan Nuwamba, sabanin dala 40.06, da aka samu a watan Oktoba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here