Gwamnatin Kano ta fara biyan mafi karancin albashi na naira dubu 71

0
28

Gwamnatin Kano ta cika alkawarin data dauka na fara biyan mafi karancin albashin ma’aikata da tace zata fara daga albashin watan Nuwamba na shekarar 2024.

Hakan ya kasance a daidai lokacin da gwamnatin ke biyan albashin ma’aikata a kowacce ranar 25 ga wata, wanda ma’aikatan suka fara ganin albashin tun daga jiya.

Gwamnatin ta roki ma’aikata da suyi amfani da karin albashin ta hanyar da zasu mori Karin, inda tace zata cigaba da inganta walwalar ma’aikatan.

Shugaban ma’aikatan gwamnatin Alhaji Abdullahi Musa, ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa gwamnatin ta kuma fara biyan bashin da ma’aikatan lafiya ke binta.

Fara biyan mafi karancin albashin ya haifar da farin ciki a tsakanin ma’aikatan sakamakon tsadar rayuwa da ake fuskanta a Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here