Matatar Fetur ta Warri zata fara aiki bada jimawa ba—NNPCL

0
29

Kamfanin man fetur na Nigeria NNPCL, ya sanar da cewa yana yin kokarin ganin matatar fetur ta Warri ta fara aiki nan bada jimawa ba.

Babban jami’in yada labaran kamfanin Femi Soneye, ne ya bayyana hakan, a yau bayan da NNPCL ya sanar da cewa matatar mai ta Fatakwal ta fara tace danyen man, bayan shafe lokaci mai tsawo ana jiran hakan.

:Yahaya Bello ya shiga hannun hukumar EFCC

Masana harkokin tattalin arziki suna kyautata zaton cewa in har aka gyara matatun an fetur mallakin gwanatin Nigeria hakan zai iya saukaka tsadar man da kuma samar dashi ba tare da yankewa ba, hadi da farfadowar tattalin arzikin kasar, da samar da ayyukan yi a tsakanin matasa.

Gwamnatin Nigeria ta mallaki matatun fetur 4 wanda baki dayan su suka dena aiki saboda gazawar gwamnatocin baya, sai da a yanzu aka sanar da kammala gyaran guda daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here