Shugaban Nigeria zai tafi kasar Faransa a gobe

0
63

Shugaban Ƙasar Nigeria Bola Tinubu, zai tafi kasar Faransa a gobe Laraba.

Mai taimakawa shugaban kasar a fannin yada yada labarai da tsare tsare, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan da yammacin yau talata, inda yace shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ne ya gayyaci Tinubu, zuwa kasar sa.

Onanuga, yace Tinubu zai shafe kwanaki uku a kasar ta Faransa, yana mai bayyana cewa za’a tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki, al’adu, da Kuma nemowa Nigeria karin wasu damarmakin cigaba musamman a fannin aikin gona, ilimi, tsaro, lafiya, da Kuma samarwa matasa aikin yi.

Haka zalika sanarwar da Onanuga, ya fitar tace shugaban Nigeria Bola Tinubu, zai yi tafiyar tare da mai dakin sa Oluemi Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here