Yahaya Bello ya shiga hannun hukumar EFCC

0
52

Tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya shiga hannun hukumar EFCC, wanda a yanzu haka yake fuskantar tuhume-tuhume kan zargin almundahanar kudaden jihar lokacin da yake Mulki.

:Sojojin Nigeria sun bukaci karin kudi saboda inganta aikin su

Jaridar Daily trust, ta rawaito cewa wasu bayanai sun nuna cewa jami’an EFCC ne suka kama shi, a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa shi ne yakai kansa ofishin hukumar tare da rakiyar lauyan sa.

Idan za’a iya tunawa hukumar EFCC ta zargi Yahaya Bello, da wawure dukiyar jihar sa lokacin da yake a matsayin gwamna, har ta yi kokarin kama shi hakan bai yiwu ba.

Bayan haka hukumar ta kai Yahaya Bello, kara gaban kotu, sannan aka jingine shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba da muke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here