Kotu ta bawa EFCC umarnin tsare Yahaya Bello zuwa ranar 10 ga Disamba

0
39

Wata babbar Kotun tarayya dake Abuja ta bawa EFCC umarnin cigaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, har zuwa ranar 10 ga Disamba.

Mai shari’ah Maryann Anenih, ce ba bayar da umarnin inda tace a ranar da za’a dawo zaman shari’ar za’a duba bukatar da aka shigar mata ta neman bayar da Yahaya beli.

:::Allah ya kare ni daga masu yi min fatan mutuwa—Obasanjo

Haka zalika kotun ta bayar da umarnin cigaba da tare mutane biyun da aka gurfanar tare da Yahaya Bello wato Umar Oricha, da Abdulsalami Hudu, wanda baki dayan su suka musanta zargi 16, da aka karanto musu na kwashe dukiyar jihar Kogi, lokacin da Yahaya Bello ke matsayin gwamna.

EFCC, wadda ta shigar da Yahaya Bello, kara itace ta roki kotu akan kar ta bayar da belin sa a yau, ta hannun lauyan hukumar Kemi Pinheiro, SAN, inda yace tun da farko wanda ake tuhuma ya bawa jami’an EFCC, wahala kafin ya mika kansa, tare da kokarin kaucewa fuskantar shari’a.

Tun da fari lauyan Yahaya Bello, Joseph Daudu, SAN, shine ya fara neman kotu ta bashi belin wadanda yake karewa, bayan sun ki amincewa da zargin tuhumar sace daukiyar jihar Kogi, tare da mallakar manyan kadarori a birnin tarayya Abuja, da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, musamman a birnin Dubai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here