Kudurin dokar haraji ta bar baya da kura a majalisar Dattawa

0
42

A yau laraba an fuskanci cece-kuce da hayaniya a majalisar dattawa lokacin da akayi kokarin tattauna batun kudirin dokar haraji da ake son yiwa gyara duk da cewa babu maganar yin nazari akan dokar a tsarin zaman majalisar na yau Laraba.

:::Kaso 40 na kanikawan mota sun rasa aiki yi a Kano saboda cire tallafin fetur

Hayaniyar ta kaure a yayin da daya daga cikin jagororin majalisar Michael Bamidele Opeyemi , ya nemi a bawa shugaban hukumar tattara haraji ta kasa FIRS, yazo ya yiwa zauren majalisar cikakken jawabi akan abubuwan dake tattare a cikin kudirin dokar harajin.

Mataimakin shugaban majalisar Barau Jibril, shine ya bayar da damar shigo da shugaban hukumar ta FIRS, don yin bayani, sakamakon cewa Barau, din ne ya jagoranci zaman majalisar dattawan na yau.

Haka ne yasa Sanata Ali Ndume, bayyana fushin sa akan hakan tare da ankarar da sauran mambobin majalisar wajen kula da ka’idar majalisar

Ndume, yace haramun ne mutane irin su shugaban hukumar tattara haraji ta kasa su shiga majalisar don yin jawabi sai dai in tun farko an shirya hakan a jadawalin zaman majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here