Yahaya Bello ya musanta zargin kwashe naira biliyan 110 na jihar Kogi

0
25

Tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya musanta zargin da hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa tayi masa na aikata laifukan almundahanar kudaden har 16, lokacin da yake a matsayin gwamnan Kogi.

:Kungiyar ASUP zata shiga yajin aiki a farkon Disamba

An gurfanar da Yahaya Bello, a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja Karkashin Mai Shari’a Maryam Anenih, tare da wasu mutane biyu da ake zargin su da aikata wasu laifukan masu suna Umar Oricha da Abdulsalami Hudu.

An zarge su da aikata laifukan almundahar kudi har naira biliyan 110.

Idan za’a iya tunawa hukumar EFCC, tun a baya take kokarin kama Yahaya Bello, bayan saukar sa daga mulkin Kogi, amma hakan yaci tura, sai a jiya talata ne ya mika kansa ga ofishin na EFCC, dake Abuja, da misalin karfe 9:45, na safiya.

EFCC, tana zargin Yahaya Bello da wawure kudin jihar Kogi, ta hanyar yin amfani dasu wajen mallakar kadarori a birnin tarayya Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here