Za’a Gudanar da Sallar Rokon Ruwa a Kasar Saudi Arabia

0
50

Mahukunta a kasar Saudi Arabia, sun nemi a gudanar da Sallar rokon ruwan sama a gobe Alhamis.

Sarkin Saudiyya Salman shine ya nemi hakan a ranar talata kamar yadda kafar yada labarai ta Arab News, ta rawaito, cewa gidan sarautar Saudiyya ya nemi gudanar da Sallar.

:::An sace buhun shinkafar tallafin Azumin Ramadan dubu 16,800, a jihar Kano

Sarkin, yace yin wannan Sallah Sunnah ce ta fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) wanda yake bayar da umarnin gudanar da sallar rokon ruwa in bukatar hakan tazo, musamman a lokacin da ake fuskantar karancin ruwa.

ya yi kiran da a yi sallar ta Istisqa, kamar yadda yake a Sunnar Annabi Muhammad (SAW), idan ana cikin buƙatar ruwan sama.

Masarautar Saudiyya ta nemi al’umma su cigaba da aikata abubuwan neman kusanci ga Allah (SWT), irin su sadaka da addu’o’i don neman rahama da saukin rayuwa da kuma jinÆ™ai daga Ubangiji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here